Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Shihab, bisa ga sabbin abubuwan da ke faruwa a fagen daga, an kai gawarwakin shahidai 6 tun daga sanyin safiyar yau zuwa asibitoci daban-daban a zirin Gaza.
A lokaci guda, wata majiya mai tushe a cibiyar likita ta Al-Shifa ta bayyana cewa, wani dan ƙasar Falasdinu yayi shahada sakamakon harbin da jiragen ruwan yakin Isra'ila suka yi a kan titin bakin teku na Al-Rashid, da ke yammacin birnin Gaza.
Majiyoyin labarai sun ba da rahoton cewa wata 'yar Falasdinu a garin Beit Lahiya da ke arewacin zirin Gaza ta yi shahada sakamakon harbin da sojojin sahayoniya suka yi mata.
Majiyoyin cikin gida na Falasdinu sun ba da rahoton kutsawar sojojin mamayar sahayoniya a sansanin "Al-Fawwar" da ke kudancin Al-Khalil a Yammacin Kogin Jordan.
Majiyoyin da aka ambata sun kara da cewa, sojojin mamaya bayan sun kutsa cikin sansanin Al-Fawwar, sun yi harbi kan 'yan ƙasar Falasdinu.
Sojojin mamayar sahayoniya sun tarwatsa tare da lalata gidajen zama da wuraren more rayuwa a gabashin Khan Yunis da ke kudancin zirin Gaza.
..........
Your Comment